IQNA

23:32 - January 31, 2017
Lambar Labari: 3481189
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kori babbar antoni janar ta kasar ta rikon kwarya Sally Yates saboda ta ki amincewa da shirinsa na korar muuslmi da 'yan gudun hijira daga kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Shafin yada labarai na kasar Amurka Lawnews ya bayar da rahoton cewa, Trump ya kori Sally Rates ne bisa a bin da ya kira yin ha'inci ga Amurka, domin kuwa taki aiwatar da umarnin shugaban kasa.

Bayanin da fadar white House ya fitar ya tabbatar da cewa alkalin alkalai na gundumar gabashin Virginia Dana Boente ne zai rike mukamin nata a halin yanzu.

Sally Rates dai ta yi watsi da kudirin Donald Trump na korar muuslmi da 'yan gudun hijira daga kasar Amurka, inda ta ce hakan ya sabawa dukkanin dokoki da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar ta Amurka, a kan ta ce in dai tana rike da wannan mukamin ba ta taba aiwatar da wannan umarni na Donald Trump ba.

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ne ya nada Sally Rates a matsayin babbar alkaliyar alkalai ta kasar Amurka ta wucin gadi.

3568716


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: