Kamfanin dilalncin labaran IQNA ya habarta cewa, Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron kasar Amurka sun kame yaron wanda yake tare da mahaifiyarsa wadda asalinta ba'iraniya ce amma haifaffar Amurka, inda suka daure shi da ankwa a cikin filin safka da tashin jiragen sama na Dalas a Virginia har na tsawon sa'oi.
Kafofin yada labarai a dukkanin fadin Amurka sun yi ta yada wannan labari, wanda hakan ya sanya kungiyoyin kare hakkin bil adama na ciki da wajen kasar suka yi Allawadai da wannan cin zarafi da muzguna wa ga karamin yaro dan shekaru 5 da sunan yaki da ta'addanci.
Sean Spicer kakakin fadar white house a lokacin da yake masa tambayoyin manema labarai, an yi masa tambaya kan wannan cin zarafi da suka yi wa wannan karamin yaro, inda ya bayar da amsa da cewa, shi ta'addanci ba shi da banbamci tsakanin babban mutum da karamin yarao.
Kama Karamin Yaro Dan Iran A Amurka Saboda Kabilanci