IQNA

22:42 - February 03, 2017
Lambar Labari: 3481198
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutanen kasar Yemen da suke zaune a birnin New York na kasar Amurka sun fito kan tituna suna nuna adawa da bakar siyasa irin ta Donald Trump.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, tashar Press TV ta bayar da rahoton cewa, mutanen da suka fito a kan titunan sun hada da ‘yan asalin kasar Yemen da kuma Amurka masu mara musu baya domin nuna wa Trump cewa ba su amince da salon siyasarsa ta wariya ba.

Wani daga cikin wadanda suka shiga jerin gwanon da ke da shagoa cikin birnin New York ya rufe shagon nasa, ya kuma rubuta abakin shagon cewa, iyalinsa suna tsare a cikin filin jirgi na New York an hana su shigowa.

A kan haka zai ci gaba da yin yajin aiki har sai an bar iyalinsa su shigo cikin kasar kamar yadda aka ba shi izinin zama, domin ba yana zaune kasar ne ba bisa kaida ba, amma sabon salon siyasar wariya da izgili da aka zo da ita yanzu a kasar na neman raba shi da iyalinsa da kuma al’ummar kasarsa ta asali.

Wasu daga cikin Amurkawan da suka shiga jerin gwanon sun sheda wa manema labarai cewa, sun shiga zanga-zangar ne domin la’antar Trump da siyasarsa da kuma wadanda suke mara masa baya kana bin da yake yi, ida suka ce wannn mutum yana neman ya rusa kasar Amurka.

A cikin makon da ya gabata ne Trump ya fara aiwatar da abubuwan da yay i alkawali a lokacin yakin neman zabe, inda y ace ya hana musulmi shiga kasar na tsawon kwanaki 90, da suka fito daga kasashen Iran, Syria, Yemen, Sudan, Libya, Iraki da kuma Somalia.

Wannan mataki dai ya fuskanci kakkausar martani daga ciki da wajen kasar ta Amurka, yayin da wasu daga cikin kasashen da lamarin bai shafe su daga cikin larabawan yankin tekun fasha suka nuna cikakken goyon bayansu ga hakan, duk kuwa da cewa bayanan da hukumomin Amurka suka fitar sun tabbatar da cewa kasashen da Trump ya ambata babu wani dan kasar da ya taba kai haria cikin Amurka, yayin da kasashen ad suke da hannu a hare-haren ta’addancin da aka kai Amurka ba su cikin wadanda dokar tasa ta shafa.

Kasar Amurka dai nta shiga cikin wani rudani da dambarwa da ba asan karshenta ba, sakamakon halin da Donald Trump ya jefa kasar, inda yake da burin ganin ya mayar da Amurka shekaru dari baya doin cimma burinsa na jari hujja.

3569986


Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iran ، Libya ، Iraki ، jari hujja ، Donald Trump ، Yemen ، New York
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: