IQNA

20:11 - February 07, 2017
Lambar Labari: 3481209
Bangaren kasa da kasa, mataimakin babban sakataren majalisar dinkin duniya kan ayyukan jin kai ya karyata rahoton da gwamnatin Myanmar ta bayar kan zarginta da ake yi da kisan musulmin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa Anatoli cewa, bayan fitar da rahoton kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar wani rahoto kan kiyashin da sojojin gwamnatin Myanmar suka yi kan musulmi, gwamnatin kasar ta fitar da wani rahoto nata kan batun.

Adama Ding mataimakin babban sakataren majalisar dinkin duniya kan ayyukan jin kaim ya bayyana rahoton na gwamnatin da cewa wani kokari na wanke daga ta’asar da aka sojojin kasar suka tafka,a kan haka ya karyata rahoton wanda gwamnatin Myanmar ta bayar kan zarginta da ake yi da kisan musulmin kasar.

A cikin rahoton da gwamnatin Mayanmar ta bayar ta ce ta gudanar da bincike kan dukkanin abin da rahoton kare bil adama na majalisar dinkin duniya ya yi ishara da shin a kisan musulmi ‘yan kabilar Rohingya a yankunan arewacin kasar, amma ba a samu wata alama da ke tabbatar da abin da rahoton kwamitin na majlaisar dinkin duniya ya bayyana ba.

A kan haka gwamnatin ta Myanmar ta kirayi majalisar dinkin duniya da a gudanar da bincike na gaskiya kafin fitar da duk wani rahoto, domin kuwa abin da aka ambata na kisan musulmi a kasar babu gaskiya a cikinsa.

Wannan rahoto na gwamnatin Myanmar dai ya fuskanci kakakusar suka daga bangarori na majalisar dinkin duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, kasantuwar rahoton ya sanawa a bin da duniya take ganin ana aikatawa akan msuulmin kasar.

3571969


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: