IQNA

23:00 - February 11, 2017
Lambar Labari: 3481221
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a birnin New York na kasar Amurka sun sanar da gayyatar mabiya addinai zuwa babban masallacin Rockland.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin lohud cewa, musulmin sun sanar da wannan gayyata ne domin bayar da dama ga wadanda ba musulmi ba da suke da rashin masaniya kan addini su fahimci hakikanin koyarwar muslunci.

Azim Faruki daya daga cikin mambobin kwamitin masallacin ya bayyana cewa, babbar manufarsu kan hakan ita ce, bayyana ma mutane hakikanin koyarwar muslunci, sabanin tunanin wasu kan muslunci inda suke kallonsa a matsayin addinin ta’addanci.

Ya ce babu abin da ya hada muslunci da ta’addanci, kuma wadanda suke aikata ta’addanci da sunan muslunci, musulmi sun fi kowa cutuwa da abin da suke yi, domin kuwa mutanen da suke kasha kullum rana da bama-bamai a kasashen yankin gabas ta tsakiya musulmi ne.

Daga karshe yace suna bayar da kyautar kwamifin kur’ani da aka tarjama a cikin harshen turanci, domin mutane su karanta da kansu su ga abin da ke cikin kur’ani.

3573148


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: