IQNA

An Kammala Taron Kungiyar Hadin Kan Jami’oin Muslunci A Ribat

23:12 - February 15, 2017
Lambar Labari: 3481232
Bangaren kasa da kasa, an kammala taron kungiyar hadin kan jami’oin kasashen musulmi karo na bakwai a birnin Ribat na kasar Morocco tare da jaddada wajabci kare jami’ar birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin ISESCO cewa, a zaman traon wanda aka kammala a jiya a birnin na Ribat, dukkanin mahalarta taron sun amince a cikin bayanin bayan taro a kan cewa dole ne a bayar da kariya ta musamman ga jami’ar Quds.

Taron wanda wannan kungiya take gudanarwa a karo na bakwai, ya mayar da hankali ne kan irin barazanar da haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya take yi wa muhimman wurare na musulmi da larabawa da ke cikin birnin Quds da nufin share su da kuma kawar da tarihinsu.

Daga ciki kuwa har da barazanar da shugaban kasar Amurka ya yi a kan cewa zai mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Quds, lamarin da ke nuni da cewa yana amincewa da birnin a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar yahudawa.

Wannan ya sanya mahalarta taron suka karfafa batun bayar da dukkanin kariya ga jami’ar birnin Quds wadda ita ce jami’a guda daya tilo da larabawa da muuslmi suke da ita a birnin, wadda take a matsayin wani gishiki na raya ilimi da al’adu na musulmi da larabawa a birnin.

Kungiyar raya harkokin ilimi da al’adun muslunci ta ISESCO ce dai ta kafa wannan kungiya ta hadin kan jami’oin musulmi, inda yanzu haka akwai jami’io 314 da suke a matsayin mambobi na kungiyar.

3574713


captcha