IQNA

22:52 - February 16, 2017
Lambar Labari: 3481236
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin makarantun jahar Carolina ta kudu a kasar Amurka ta sanar da cewa za ta koyar da addinin muslunci ga dalibai.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na « postandcourier» Ryan Brown kakakin majalisar dokokin jahar Carolina ta kudu ya bayyana cewa, wannan tsarin bai sabawa kaidar koyarwa a jahar ba.

Ya ce babban abin da ake bukata ga dalibi shi ne ya zama yana da masaniya a kan abubuwa daban-daban, da hakan ya hada da al'adu na wasu mutane da yanayin addininsu, wanda hakan ba yana nufin sanya dalibi a cikin wannan addini ko alada.

Wannan bayani ya zo ne sakamaon nuna rashin amincewar da wasu mahaifan daliban suka nuna da hakan, musamman ma da suka ji cewa za a koyar da akidun muslunci ga dalibai, inda suke ganin cewa cewa tamkar za a sanya tasirin muslunci a cikin zutan yaynsu.

Brown ya kara da cewa tun kafin wannan lokacin ana koyar da ilimin sanin akidun addina kamar kiristanci da yahudanci a makarantun jahar, saboda haka shi ma addinin muslunci za a koyar da akidunsa ne a matsayin wani bangare na ilimi kawai ba domin yada muslunci ko neman wani ya shi muslunci ba, domin su kansu wadanda za su koyar ba musulmi ba ne.

3575098


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: