IQNA

23:29 - February 19, 2017
Lambar Labari: 3481245
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a a birnin Baltimore na jahar Maryland a kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin «icnaconvention» cewa, wannan gasa za a gudanar da ita ne a lokacin babban taron musulmin karo na arbain da biyu da za a gudanar a garin Baltimore.

Bayanin ya ci gaba da cewa, manyan kungiyoyin musulmi na Amurka za su halarci zaman taron da suka hada da (ICNA)da kuma (MAS) da sauransu.

Malami da kuma masana daga cikin musulmin kasar ta Amurka za su gabatar da jawabai a kan batutuwa da daban-daban da suka shafi addinin muslnci, musamman ma a wannan lokaci da kasar Amurka take ganin wasu sauye-sauye da bata taba ganin irinsu ba, inda gwamnati da kanta ke nuna wariya da kyama a kan musulmi da ma wasu jinsi da na Amurka ba a hukumance.

A bangaren kara yara ‘yan kasa da shekaru 10 za su kara da juna, a bangaren harda kuwa ‘yan shekaru 12 da kuma shekaru 14 sai kuma yan shekaru 16 su ne za su kara da juna a gasar.

3576156


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: