IQNA

Jagoran Juyin Islama:
23:48 - February 21, 2017
Lambar Labari: 3481250
Bangaren siyasa, Ayatollah sayyid Ali Khamanei jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyana cewa, za su ci gaba da goyon bayan masu gwagwarmaya domin neman ‘yanci daga daga mamamayar yahudawan sahyuniya, da kuma tsarkake wuraren musulunci masu tsarki daga mamayar yahudawa ‘yan kaka gida.

Kamfanindillancin labaran IQNA ya habarat cewa, an bude babban taron kasa da kasa domin taimakon intifadar falastinawa karo na shida a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran a safiyar yau Talata.

Kamar dai sauran tarukan da suka gabata, a wannan karon ma jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah sayyid Ali Khamenei ne ya jagoranci bude zaman taron taron, inda ya gabatar da jawabinsa ga mahalarta taron, da suka cika babban dakin gudanar da manyan taruka na kasa da kasa da ke birnin Tehran.

Baki kimanin dari bakawai ne daga kasashe tamanin suke halartar taron, da suka hada da shugabannin majalisun dokoki na wasu daga cikin kasashen msuulmi da kuma na larabawa, gami da masana musulmi da ma wadanda ba musulmi, da jagororin kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa.

A cikin jawabinsa a wurin taron, jagoran juyin Islama Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada matsayin jamhuriyar musulunci ta Iran na ci gaba da bayar da dukkanin taimako ga al’ummar palastine da kuma gwagwarmayar da suke yi domin kwatar ‘yancinsu daga mamaya da zaluncin yahudawan sahyuniya.

Jagoran ya bayyan palastinawa ‘yan gwagwarmaya amatsayin jagororin neman ‘yancin Palastinu, kamar yadda ya bayyana su a matsayin jagororin gwagwarmaya a yankin, inda ya ce hakika tsayin dakan da falastinawa ‘yan gwagwarmaya suka yi a Gaza a gaban yahudawan sahyuniya, da kuma tsayin daka da turjjiya da yahudawan sahyuniya suka fuskanta daga masu gwagwarmaya a Lebanon, hakan shi ne babban abin da ya rusa shirin fadada mamayar Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.

Dangane da sabbin makirce-makircen da yahudawa da iyayen gidansu suke shirya ma al’ummar musulmi a yankin gabas ta tsakiya kuwa, musamman ma dai gungun masu gwagwarmaya a yankin, jagoran ya yi hannunka mai sanda da cewa ya zama wajibi a zama cikin fadaka, domin kuwa a kowane lokaci makiya al’umma suna yin amfani hanyoyi daban-daban, da kuma mutane daban-daban da gwamnatoci daban-daban domin cimma manufarsu, wanda kuma ko shakka babu ta hakan suke son su yi amfani da wasu a yankin gabas ta tsakiya domin raunana wani bangaren gwagwarmayar Palastine, inda ya ce gwagwarmayar neman ‘yanci da yaki da zaluncin yahudawan sahyuniya ba za ta yi rauni ba, domin kuwa idan wani bangare ya ja da baya, wani bangaren kuma zai kara kumaji da zage dantse, kuma Iran za ta yi mu’amala ne da duk wanda ya sabi tutar yaki da zallunci da mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Palastinu da kuma sauran kasashen musulmi.

A wani bangaren jawabin nasa jagoran ya yi ishara da yadda makiya suka ci nasara a wani bangare na makircin da suke shirya ma al’ummar muuslmi, musamman batun palastinu da mamayar da yahudawan sahyuniya suke yi a kanta da sauran wurare masu tsarki, inda suka yi amfani da wasu daga cikin gwamnatocin yankin gabas ta tsakiya da wasu sarakuna domin cimma wannan buri, inda a halin yanzu za mu ga cewa sun shagaltar da musulmi da junansu, ta yadda a yau musulmi sun manta da wane ne makiyinsu na hakika, sun koma suna kallon junansu a matsayin makiya, alhali shi makiyin musulmi babu wani banbanci a wurinsa a tsakanin musulmi, matukar suna karba sunan musulmi.

Daga cikin wannan makirci kuwa har da yadda aka yi amfani da wasu daga cikin irin wadannan gwamnatoci da sarakuna na kasashen yankin gabas ta tsakiya wajen kirkiro kungiyoyin ‘yan ta’adda, suna yin aikin da ya kamata a ce Isra’ila ce take yin sa da kanta, amma sai Isra’ila ta koma inuwa tana hutawa, su kuma suna yi mata wannan aiki na rusa kasashen musulmi da kasha dubban musulmi da tayar da bama-bamai duk da sunan jihadi a tafarkin addinin musulunci.

Baya kammala jawabin na jagora, wasu daga cikin manyan baki sun gabatar da jawabi, da suka hada da shugaban kungiyar Jihadul islami Ramadan shallah, da kuma shugabannin majalisun dokoki na kasashe daban-daban, kamar yadda kuma mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’in kasim ya gabatar da jawabinsa a madadin kungiyar.

Taron dai yana ci gaba da gudana, inda dukkanin jawaban da aka gabatar kuma a ke ci gaba da gabatarwa a wurin taron, suna jaddada wajabcin ci gaba da mara baya ne ga intifadar al’ummar Palastine, domin ci gaba da gudanar da gagarumin aikin da suke yi a madadin al’ummar msulmi baki daya, na kare kasar musulmi da kuma wurare masu tsarki na musulmi da ma sauran addinai da aka safkar daga sama da suke fuskantar baranaza keta hurumi daga yahudawan sahyuniya.

3576729


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: