IQNA

23:50 - February 21, 2017
Lambar Labari: 3481251
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin ‘yan was an fina-finai a Amurka wanda shi ma musulmi ne ya bayyana cewa babu wani abin mamaki kan nuna wa musulmi bakar fata banbanci a Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Guardian cewa, Ali wani dan kasar Amurka ne wanda ya sheda wa jaridar Time scewa, musulmi sun saba ganin banbanci da nuna musu wariya a kasar Amurka.

Ya ce babu wani abin mamakia cikin hakan, abin mamakin dai kawai shi ne a halin yanzu nuna kyama ga musulmi a kasar gwamnati ce take yin hakan a hukumance, sabanin lokutan baya inda wasu mutane ne kawai suke yin hakan amma ba sunan doka ba.

Mahir Shala Ali mahaifiyarsa ta kasamce babbar malamar addinin kirista, kuma ta karbi addinin muslnci a cikin shekara ta 1999 a kasar.

Ya karbi lambobin yabo har sau 25 a fina-finai daban-daban da ya fito, kamar yadda kuma awannan karon yana daga cikin mutanen da ake sa ran za su samu kyautar fina-finai ta Oscar a kasar ta Amurka.

Ali ya ce sakamakon salon siyasar da sabuwar gwamnatin kasar ta dauka na kin musulmi, wannan ya sanya bangarori da daman a Amurka bas u amince da siyasar kasarsu ba a halin yanzu, inda hatta hukumar fina-finai ta Hollywood tana shirin daukar matakin kalu balantar Trump nan ba da jimawa ba.

3576764

Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، oscar ، Amurka ، hollywood ، fina-finai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: