IQNA

23:36 - February 23, 2017
Lambar Labari: 3481255
Bangaren kasa da kasa, wasu mata a garin Fort McMurray na kasar Canada sun nuna goyon bayansu ga mata msulmi da ake takura mawa saboda saka hijabi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin kamfanin dillancin labarai na Anatoli na kasar Turkiya cewa, a cikin wannan wata da muke ciki ne sakamakon nuna takura ma mata masu saka hijabi da ake yia wasu yankuna na kasar Canada gungun wasu mata da ba msuulmi suka nuna goyon bayansu ga mata msuulmi.

Sakamakon karuwar masu kin jinin muslunci a cikin wasu kasashen turai da kuma Amurka a halin yanzu da hakan ya zama a hukumance, musulmin kasar Canada suna ganin tasirin hakan a kasar, domin kuwa a cikin ‘yan makonnin bayan rantsar da shugaban Amrka, an kai hare-hare a kan masallatai da cibiyoyin addinin muslunci a garurwa daban-daban na kasar.

Mata musulmi masu saka hijabi su ne suka fi fuskantar matsaloli daga masu kyamar musulunci sakamakon lullubin da suke yi a kansu,wanda hakan ya sanaya wannan kungiya ta mata a garin na Fort McMurray nuna goyon bayansu ga mata musulmi, inda mambobin wannan kungiya wadanda mabiya addinin kirista suka kwashe wata guda suna saka lullubi irin na mata musulmi domin su nuna goyon bayansu ga ‘yan uwanssu mata da ake tozartawa saboda akidarsu ta addini.

3577543

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: