IQNA

23:29 - February 27, 2017
Lambar Labari: 3481268
Bangaren kasa da kasa, Kotun masarautar Bahrain ta sake dage zaman sauraren shari'ar da ta ce tana gudanarwa a kan babban malamin addinin muslunci na kasar Sheikh Ayatollah Isa Kasim.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin jaridar Mir'ar Bahrain ya bayar da rahoton cewa, kotun masarautar kasar ta Bahrain ta sanar da cewa, ta dage zaman yanke hukunci a kan Sheikh Kasim zuwa ranar 14 ga watan maris mai kamawa.

Kafin wannan lokacin da alkalin alkalan masarautar Bahrain, ya sheda cewa za a yanke hukunci na karshe a kan sheikh Isa Kasim.

Gidan sarautar bahrain na zargin Sheikh Ayatollah Isa Kasim da goyon bayan 'yan adawar siyasa a kaar, wadanda suke nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin masarautar kasar.

A kan wannan dalili masarautar ta sanar da janye izinin zama dan kasa a kan malamin, wanda shi ne ya fi kowa yawan mabiya a kasar, tare da bayar da umarnin a fitar da shi daga daga lasar, amma hakan ta faskara, domin kuwa al'ummar kasar Bahrain sun sha alwashin kare rayuwar shehin malamin har zuwa karshen lumfashinsu.

3578769

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: