Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin bawabah news cewa, Khalid Nushi shugaban hukumar sanya ido kan buga littafai ta kasar Masar ya sanar da cewa, sun kai samame a wata madaba’anta a yankin Alsalam da ke birnin Alkahira.
Ya ce sun kai samamen ne bayan samun bayanai dangane da buga kur’ani da kuma wasu littafai da aka yi a wurin ba tare da samun izini daga bangaren da ke bayar da izini na cibiyar Azhar ba.
Ya ce daga cikin abubuwan da suka kwacea wannan wuri har da kwafin kur’ani mai tsarki kimanin guda dubu 40, duk kuwa da cewa babu wani kure a cikin bugun da aka samu, to kuma ba a bi ka’idar da ta dace ma a hukumance wajen aikin bugun kur’anan.
Domin kuwa a cewarsa wannan aiki ya sabawa ayar doka ta 102 da ke cikin kundin tsarin buga littafai ta kasa da aka rubuta a shekara ta 1985.
Ya kara da cewa, ko shakka babu gwamnatin masar tana kallon irin wannan aiki a matsayin aiki mai matukar hadari, domin kuwa buga littafai ba tare da izini ba, zai iya haifar da matsaloli da za su kawo rashin jituwa a tsakanin al’umma, musamman kur’ani wanda kure wajen buguga shi yana tattare da gagarumin hadari.