Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin tashar Russia Today cewa, cibiyar yada al’adun muslunci ta birnin London da ke karkashin kulawar masarautar Saudiyya ta shirya wani shirin bayar da horo na watanni 5 da harshen farisanci da sunan koyar da tafsirin kur’ani mai tsarki.
Wannan shiri dai ya gudana tare da halartar matasa daga kasashen da suke fahimtar harshen farisanci, babbar manufar shirin dai ita ce kara jawo hankulan matasa musulmi zuwa ga akidar wahabiyanci amma da sunan koyar da su tafsirin kur’ani mai tsarki.
Tun kafin wannan lokacin dai cibiyoyin da ke daukar nauyin yada akidar wahabiyanci a Saudiyyah, sun tashi haikan wajen ganin sun mamaye dukkanin cibiyoyi da masallatai na musulmi da suke cikin kasashen turai, da nufin yada akidar wahabiyanci, kuma suna yin hakan ne tare da hadin gwiwa da gwamnatocin kasashen turan.
Bayan shudewar wani dan lokaci, da dama daga cikin kasashen turan sun fara kokawa kan irin akidun da ake koyarwa a wadannan wrare, domin kuwa daga nan ne ake samar da matasa masu dauke da akidar takfiriyya, wadanda kuma su ne ke zama ‘yan ta’adda masu kai hare-hare da sunan jihadi.
Daya daga cikin dalilan da wasu gwamntocin turan suka bayar kasashen Jamus da Holand shi ne, dukkanin ‘yan ta’addan da suka tafi kasashen Syria da Iraki suka hade da sauran ‘yan ta’adda na IS sun fito ne daga wadannan cibiyoyi da ke karkashin kulawar Saudiyyah a cikin kasashensu, wanda hakan neyasa suka fara rufe irin wadannan cibiyoyi na wahabiyawa da nfin rage kaifin yaduwa akidar ta’addanci da ta samo asali da tushe daga wahabiyanci.
Sakamakon yaduwar wannan akida ne kyamar addinin muslunci ta karu a cikin kasashen turai, inda da dama daga cikin turawa suke yi dukkanin musulmi irin wannan kaloo, musamman ganin cewa kasar da msulmi ke kallonta amatsayin abin koyi it ace kuma take kan gaba wajen daukar nauyin ta’addanci da sunan addinin muslunci ko kuma sunnar manzo mai tsira da aminci.
Yanzu haka wannan cibiyar muslunci ta ta koma ta wahabiyanci da ke birnin London da aka gina a shekara ta 1944 kuma aka gyara ta a 1978, tana shirin sake gudanar da wanin shirin bayar da horoa cikin harsunan larabci, turanci, yaren Holland, Kurdanci da kuma harshen Hausa.