Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzio na Iina cewa, a daren yau ne za a bude wani babban taro na kasa da kasa kan irin rwar da kafofin yada labarai suke takawa wajen warware rashin fahimta atsakanin mabiya addinai.
Wannan taro dai zai mayar da hankali ne kan irin yadda ya kamata kafofin yada labarai su yi amfani da kwarewarsu wajen isar da sakon zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin jama’a.
Masana daga kasashen duniya za su gabatar da jawabai a wurin wannan taro, kan batutuwa da suka shafi yadda ake amfani da wasu kafofin yada labarai domin yada akidar ta’addanci, da kuma yadda ya kamata sauran kafofin yada labari su fuskanci wannan lamari.