IQNA

Sunan Fatima Na Saurin yaduwa A kasar Finland

23:38 - April 01, 2017
Lambar Labari: 3481365
Bangaren kasa da kasa, sunan Fatima na saurin yaduwa a tsakanin sunayen jarirai mata a kasar Finland.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wani bincike ya yi nuni da cewa, harshen larabci na a matsayin harshen a uku da aka fi Magana da shi a kasar Finland a halin yanzu.

Rahoton ya ce, akasarin musulmi da kma larabawa da ske zaune a kasar, suna saka ma yaransu jairai mata sunan Fatima fiye da kowane suna.

Kasar Finland dai tana daya dga cikin kasashen da suke gabashin nahiyar turai, wanda kuma ta kasance ta tasirantu matuka da harshen rashanci da kuma Istuwaniya, inda a halin yanzu kuma saboda yawan amasu gudun hijira larabawa a kasar, larabci yana a matsayin harshen a uku.

Yawan gudun hijira a tsakanin kasashen larabawa da ke fama da tashin hankali ya karu nea cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan sakamakon rikice-rikicen da aka haddasa a cikin kasashen larabawan saboda da dalilai na siyasa.

Duk da cewa akwai kasashen da suke da makudan kudade da za su iya daukar nauyin dukkanin larabawan da suka yi gudun hijira, amma ba su yi hakan ba, duk kuwa da cewa kasashen larabawa mafi arziki su ne suke daukar nauyin dukkanin tashe-tashen hankula da kuma dukar nauyin ‘yan ta’adda a kasashen larabawa da ake fama da ta’adanci.

3586254


captcha