Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban jami’in da ke kula da ayyukan sake gyara haramin Makka mai alfarma ya bayyana cewa, an kammala kusan kashi 90 cikin dari na dukkanin ayyukan da suka shafi gini.
Ya ce abubuwan da suka yi saura sun shafi ayyukan wutar lantarki ne da kuma saka alamu na musamman a cikin wurin, gami da lasifikoki.
Dangan da fitar wuraren dawafi da kuma wuraren tsayuwa domin salla, ya ce dukan kammala ayyuka da suka danganci hakan, kuma nan ba da jimawa ba ake sa ran za a kammala sauran ayyukan baki daya.