Nurul Haq wani mahardacin kur'ani ya sheda wa kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ana shirin gudanar da wata babbar gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Ghana.
Ya ci gaba da cewa wannan gasa za ta kunshi yara 'yan shekaru 11, 15, 16 zuwa 20 da kuma 'yan kasa da shekaru goma da haihuwa, kuma gasar za ta kunshi bangaren mata da maza.
Yahuza ya kara da cewa, wannan gasa za ta gudana ne a birnin Akra babban birnin kasar, inda za a kasa gasar zuwa bangarorin karatu da kuma harda.
Za a kammala gasar ne kafin kammala azumin watan ramadan, inda za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazoa gasar, bayan bada kyautuka na bai daya ga dukkanin wadanda suka halarci gasar.
Yanzu haka babbar cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani ta kasar ta kammala mafi yawan shirye-shryen da suka kamata domin shirya wannan gasa, wadda za ta samu halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar.
3588322