IQNA

Kungiyar Ta'addancin Daesh Ta Dauki Nauyin Harin Masar

20:37 - April 10, 2017
Lambar Labari: 3481394
Bangaren kasa da da kasa, kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta dauki alhakin kai hare-haren da sukayi sanadanin mutuwar mutane akalla arba'in da uku a wasu majami'i biyu na Masar a safiyar jiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin elwehdah.com cewa, an kai harin ne lokacin da Kiristoci Kifdawa ke bikin Palm Sunday, daya daga cikin ranaku mafiya tsarki a addinin Kirista, domin tunawa da galabar da Almasihu ya samu ta sake shiga birnin mai alfarma.

Harin mafi muni shi ne wanda ya yi sanadin mutuwar mutane ashirin da bakawai tare da raunana wasu a cocin kifdawa ta birnin Tanta, sai kuma na cocin Alexandria da ya hallaka mutane sha shidada raunana wani adadi mai yawa.

Wadanne hare-haren na zuwa ne a kasa da kwanaki sha tara kafin ziyara da ake sa ran Paparoma Faransis na mabiya darikar Katolika zai soma a kasar ta Masar daga ranar ashirin da takwas na watan nan.

Gwamnatin Masar dai ta bakin firaministan ta sherif Ismaïl ta yi Allah wadai da hare-haren tana mai kara jadadda ci gaba da yakar ayyukan ta'addanci tun daga tushensu.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba a ake kai hari makamancin hakan a wannan kasar ta Masar ba inda ko a watan Disamba bara wani makamacinsa ya yi sanadin mutuwar mutane ashirin da tara a mujami'un Saint-Pierre da kuma Saint-Paul dake Alkahira babban birnin kasar.

3588616

captcha