Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau an fara gudanar da wannan gasar kur'ani mai tsarki tare da halartar makaranta 120 daga kasashe 69.
Bayanin ya ce tuni makarantan da mahardatan suka halarta, inda a yau aka gudanar da taron bude gasar, wanda kuma za ta ci gaba daga nan har zuwa mako guda.
Daga Iran an samu halartar Mujtaba Muhammad Bigi a bangaren karatu da kuma hardar dukkanin kur'ani mai tsarki, kamar yadda kuma Dawud Fallahi shi ma daga Iran, zai shiga bangaren hardar dukkanin kur'ani mai tsarki.
A shekarar da ta gabata Ibrahim Fallah Tabassum Chehreh tare da Muhamamd Mahmudi ne suka wakilci kasar Iran a gasar kur'anin ta duniya a Kuwait a karo na bakawai, inda Ibrahim Fallah Tabassum Chehreh ya samu nasarar zuwa na uku a gasar, yayin da shi kuma Muhammad Mahmudi bai samu zuwa nasarr samun matsayin da ake bukata ba, wata na daya ko na biyu ko kuma na uku.
Bayan kammala wannan gasa dai za a bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, kamar yadda kuma ake bayar da kyautuka da suka kebanci wadanda suka nuna kwazo tare da samu matsayin na makin da ake bukata.
3587801