IQNA

Jordan Ta Hana Raba Wani Kwafin Kur'ani Na Saudiyya A Kasarta

22:04 - April 18, 2017
Lambar Labari: 3481417
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Jordan ta hana raba wani kur'ani da aka buga akasar saudiyyah saboda wasu kura-kurai wajen bugunsa.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Eram News cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Jordan ta bayar da umarnin tattara wani kwafin kur'ani da aka buga a ksar Saudiyya bayan gano wasu kura-kurai na wasali.

Cibiyar ayyukan gaji da taimakon jama'a ta Hashimiyyah ta kasar saudiyya ce dai ta dauki nauyin buga wannan kwafin kur'ani tare da rarraba shi ga jama'a a cikin kasar ta Jordan.

Daga kurakuran da aka gano har yin wasali na fataha a kan Kalmar sunan Allah wato lafazin Jalalah mai tsarki, a cikin aya ta 11 a cikin surat Luqman a shafi na 207, inda maimakon fataha a kan lafazin zai aka yi wasali kasa ko kuma kasra.

Abin tuni dais hi ne ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Jordan ita ce ke da alhakin sanya ido a kan duk wani abin da za a shigo da shia cikin kasar da ya danganci littafai na addini, kuma ita ke hakkin bayar da izinin raba su ko kuma hana yin hakan.

3590794
captcha