Musa Jida a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran IQNA ya yi bayani dangane da wani abu da ya shafi rayuwarsa:
Ko z aka yi mana bayni dangane kanka, daga wane gari ne na kasar Kamaru kake?
Sunana Musa Jida dan shekaru 18, daga garin Kusri na kamaru.
An haifeka da makanta ne ko kuwa daga baya ta sameka?
Bani da matsalar makanta a lokacin da aka haife ni, amma ta same ni ne ina da shekaru biyar da haihiwa.
Daga wace shekara ka fara hardar kur'ani?
Tuna shekarar 2013, mahaifina ne ya karfafa mani gwiwa, kuma na yi karatun kur'ani ne a Najeriya, amma yanzu ina wakiltar Kamaru.
Kat aba hakartar wata gasa ta makafi kafin wannan gasa ta Iran?
A'a, ban taba halartar wata gasa ba a rayuwa ta.
Ya gasar Iran ta kasance?
Ta yi kyau matuka, ban samu wata matsala ba.
Su wane ne malamanka na kur'ani?
Sheikh Umar Alamin shi ne malamina na farko, sai kuma wasu malaman kamar Abdullah man Harun.
Wadannan malamai sun rika bani ayoyi biyar-biyar ina hardacewa , da hakan har na hardace kur'ani.
Ka tab ahalartar wata cibiya somin koyon hardar kur'ani?
A'a, ban taba halartar wata cibiya ba, a gida na koyi harda malamaina suna kara mani har na hardace.
3595323