IQNA

An Girmama Makarancin Iraki Da Ya Halarci Gasar Kur’ani Ta Makafi

22:36 - May 03, 2017
Lambar Labari: 3481460
Bangaren kasa da kasa, Irakawa da dama suka taru domin taya dan kasar murna wanda ya samu nasara a gasar kur’ani ta duniya ta makafi da aka gudanar a Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin qaf cewa, an gudanar da taron ne a garin Diwaniyya na kasar Iraki, inda aka girmama Muhammad Abdulshahid Baqer, makarancin da ya zo na a matsayi na uku a gasar kur’ani ta makafi a Iran.

Sheikh Amjad Alhasnawi shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin kur’ani mai tsarki a garin Diwaniya wanda kuma shi ne ya shirya wannan taro na girmama wannan makaranci.

Haka ann kuma an samu halartar wasu daga cikin fitattun makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki na kasar Irakia wurin wannan taro, da suka hada Sajjad Amir, da kuma Ali Khaffaji, sai kuma Ahmad Kazem, wadanmda fitattun makaranta kur’ani ne na kasar Iraki.

3595797


captcha