IQNA

Rufe Cibiyoyi 16 Na Kur'ani A Madagaska

21:07 - May 06, 2017
Lambar Labari: 3481489
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar ilimi a kasar Madagaska ta sanar da cewa za ta rufe wasu cibiyoyin kur'ani guda 16 a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na almisriyun cewa, ma'aikatar ilimi ta kasar Madagaska ta sanar da cewa, za ta rufe wasu cibiyoyin ilimi guda 16 a kasar wadanda ake koyar da kur'ani a cikinsu.

Poul Ribari ministan ilimi na kasar ta Madagaska ya bayyana cewa, sun dauki wannan matakin ne sakamakon saba kaida da wadannan cibiyoyi suka yi bisa dalilan gina su.

Ya ce wadanann cibiyoyi an gina su da sunan cibiyoyin karatun kur'ani, amma daga bisani kuma sun koma suna bayar da horo a kan kur'ani ga jama'a, sabanin yarjejeniyar da aka yi da su tun daga farko.

A kan haka ya ce, zai gana da shugabannin musulmi a kan wannan batu, kuma za a aiwatar da shirin dakatar da wadannan cibiyoyin ne bayan karewar zangon karatun da ake ciki a halin yanzu.

Tsakanin karni na shida zuwa na tara ne musulunci ya shiga tsibirin Madagaska da ke kudu maso gabashin nahiyar Afirka, kuma kididdiga ta 2010 ta yi nuni da cewa adadin musulmi a lokacin ya kai dubu 220, wanda kuma adadin yake ci gaba da karuwa.

3596267
captcha