Bayanin malaman ya bayyana hakan a matsayin cin amana ga al'ummar musulmi na Palastinu, wadanda yahudawan Isra'ila ke yi wa kisan gilla a kullum rana ta Allah, tare da kiran masarautar kasar da ta sake yin nazari a hankoronta na kulla kawance da Isra'ila.
Su a nasu bangaren dubban jama'a da suke gudanar da zaman dirshan a kofar gidan babban malamin addini na kasar Ayatollah Isa Kasim, sun yi ta rera taken yin Allawadai da karbar bakuncin tawagar yahudawan Isar'ila da masarautar kasar Bahrain ta yi, tare da bayyana haka a matsin babban cin amana ga al'ummar Palastinu da ma sauran musulmi da larabawa.