IQNA

An Bude Dakin Watsa Shirye-Shiryen Kur'ani A Hubbaren Imam Hussain (AS)

22:50 - May 11, 2017
Lambar Labari: 3481503
Bangaren kasa da kasa, a yunkurin ganin an samu damar gudanar da ayyukan kur'ani na sha'abaniyya an bude wani dakin watsa shirin kur'ani daga hubbaren Imam Hussain (AS)

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na hubbaren Imam Hussain (AS) cewa, an kaddamar da wannan dakin watsa shirye-shiryen kur'ani mai tsarki domin daukar ayyukan darararen sha'abaniyya.

Taron kaddamarwar dai ya samu halartar Sayyid Said Muslim da Ahmad Abdulhayyi, fitattun makaranta kur'ani mai tsarki daga kasar Masar, gami da Ustaz Hassan almansuri, shugaban cibiyar kur'ani ta wannan hubbare mai tsarki.

Jama'a da dama ne dai suka taru a wurin, inda aka gabatar da bayanai da kuma kira'ar kur'ani mai tsarki daga fitattun makaranta na ciki da wajen kasar ta Iraki.

Sayyid Saeed Muslim ya bayyana cewa, babbar manufar bude wannan dakin watsa shirye-shiryen kur'ani dai ita ce kara fadada lamarin kur'ani mai tsarki a tsakanin mabiya ahlul bait (AS) da sauran al'ummar musulmi na kasar Iraki, wanda ko shakka babu hakan yan ada babban tasiri a cikin zamantakewa irin ta musulmi.

Daga cikin abubuwan da za a rika gudanarwa har da watsa karatun manyan makaranta, da kuma dauko shirye-shirye da suka danganci tarukan kur'ani da watsu su kai tsaye daga wanann huri da ke hubbaren Imam Hussain (AS), tare da bayar da dama ga malaman kur'ani su gabatar da jawabai da suka danganci ilmomin wannan littafi mai tsarki.

3598037


captcha