IQNA

An Gurfanar Da Wata Mata Bisa Laifin Cin Zarafin Musulmi A Australia

23:18 - May 12, 2017
Lambar Labari: 3481507
Bangaren kasa da kasa, an gurfanar da wata mata a gaban Kuliya bisa laifin cin zarafin wasu daliban jami'a mata musulmi a garin New South Wales na kasar Australia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Guardian ta bayar da rahoto a shafinta na yanar gizo cewa, wata kotu a birnin New South Wales na kasar Australia ta gurfanar da wata mata wadda ta kai farmaki a kan wasu daliban jami'a mata msuulmi da suke sanye da lullubi a gaban jami'ar birnin.

Hanan Marhab wadda daya ce daga cikin daliban ta bayyana cewa, bayan sun kammala darasi a cikin jami'a sun fito su hudu tare da kawayenta da nufin tafiya gida, ba zato babu tsammani sai wannan matar ta kai mata farmaki tare da fasa mata baki, sannan kuma ta haura a kan sauran kawayenta da duka, a nan take dai masu gadin jami'ar suka kama ta tare da mika ta ga jami'an tsaro.

Musulmin kasar Australia na fuksnatar barazana da cin zarafin daga wasu ‘yan kasar masu tsananin kyamar addinin muslunci, duk kuwa da irin matakan da gwamnatin kasar take dauka wajen nuna rashin amincewar da hakan.

3598426


captcha