Shafin yada labarai na Manama Post ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyin farar hula da kuma jam’iyyun siyasa a kasar Bahrain sun nuna rashin amincewarsu da shirin masarautar kasar na neman kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila.
A cikin bayani na da kungiyoyi da jam’iyyun siyasar suka fitar, sun bayyana shirin masarauatr da cewa yana a matsayin cin amanar al’ummar Palastinu da ma musulmi baki daya, domin kuwa al’ummar Bahrain ba ta taba amincewa da samuwar Isra’ila ba, kuma hankoron yin hakan daga mahukuntan kasar ba abu ne da za a amince da shi ba.
Haka nan kuma bayanin ya nuna goyon baya ga fursunonin Palastinawa da suke tsare a gidajen kason haramtacciyar kasar Isra’ila da suke yajin cin abinci.
Kamar yadda kuma bayanin ya kirayi dukkanin kasashen musulmi da ma kasashe masu ‘yancin siyasa, da su mara baya ga al’ummar palastinu musamman fursunoni masu yajin cin abinci, domin tilasta haratacciyar kasar Isra’ila da ta saurari bukatunsu.
Tun sama da makonni uku da suka gabata ne fursunonin palastinawa da suke tsare agidajen kurkukun Isra’ila su kimanin dubu daya da dari takwas suka shiga yajin cin abinci, domin nuna rashin amincewarsu da halin da suke ciki na kunci a wuraren da ake tsare da su.