IQNA

A Jiya Ne Aka Bude Gasar Kur’ani Ta Duniya A Kasar Malaysia

23:17 - May 16, 2017
Lambar Labari: 3481519
Bangaren kasa da kasa, a jiya ne dai aka bude gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya karo na 59 a kasar Malaysia.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya bayar dar rahoto daga birnin Kualalampour cewa, a jiya ne aka gudanar da bukin bude gasar ta 59 da kimanin kaarfe 20:00 agogon kasar, wato karfe 16:30 agogon Tehran, a babban dakin taron PWTC, tare da halartar minister mai kula da harkokin addini na kasar tare da halartar baki ‘yan kasa da manyan jami’an gwamnati gwamnati gami da sauran baki.

Jim kadan baya fara bukin bude taron sn fara gudanar da karatu wadanda suka fara gudanar da gasar su ne, Taha Izzat Bisyuni dan shekaru 13 daga Masar, sai kuma Khairu Nisa Hasani Ajas, daga Indonesia, daga nan kuma sai Muhsana bint Yusuf daga Myanmar.

Bayann kuma Ilyals Kiliar daga Spain, sai kuma Muhamidin Aumfogh daga Phalipines, Yusuf Abduv daga Rasha sun gudanar da nasu karatun a wajen bude wannan babbar gasar kur’ani ta duniya.

Sai dai wadanda suke bin diddigin lamarin suna kallon sanya karamin yaro da ba shi da gogewa wajen karatu na kasa ya zama wanda zai bude gasar yana amatsayin rashin kyautatawa gag a mahalarta taron, inda ake ganin da ya kamata a sanya fitattun makaranta da suka kware suka goge domin abin ya yi armashi yadda ya kamata.

Haka nan sanya masu karatu daga kasashen RTasha da Spain wadanda sum aba su da gogewa, yana nuna rashin samun kyakkyawan tsari daga masu shirya wannan gasa a wannan shekara, inda ake ganin ya kamata a dauki darasi daga abin da ya faru na rashin gudanar lamarin yadda ya kamata domin kada a sake maimaita hakan a gaba.

Hamid Alizadeh daga Iran ya gabatar da karatun kur’ani mai tsarkia yau a r4anar farko ta bude wannan babbar gasa ta kasa da kasa a kasar Malaysia, wadda za ta kawo karshe a ranar Juma’a mai zuwa, makaranta kur’ani 24 ne daga kasashe 24 za su kara da juna da kuma makaranta mata guda 10 a gasar ta Malaysia, kamar yadda a bangaren harda maza 20 ne da kuma mata goma.

3599896


captcha