IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Harin Kiristoci A Afirka Ta Tsakiya

21:56 - May 17, 2017
Lambar Labari: 3481523
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen msuulmi ta yi Allawadai da harin da yan bindga kiristoci suka kaddamar a kan musulmi a garin Bangassou da ke cikin jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar kasashen msuulmi ta bayyana harin da yan bindga kiristoci suka kaddamar a kan musulmi a garin Bangassou da ke cikin jamhuriyar Afirka ta tsakiya da cewa aiki ne na dabbanci da kuma neman haddasa husuma tsakanin mabiya addinan biyu.

Kakakin dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya sanar da cewa: Daruruwan 'yan dabar kungiyar kiristoci da suka mamaye garin Bangassou da ke shiyar kudu maso gabashin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun janye daga garin.

Kakakin dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Herve Verhoosel ya bayyana cewa; Daruruwan 'yan dabar kungiyar kiristoci masu dauke da makamai a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun fice daga garin Bangassou da suka mamaye bayan kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan garin tun daga ranar Juma'ar da ta gabata.

Tun a ranar Juma'a da ta gabata ce gungun 'yan dabar kungiyar kiristoci ta Anti-Baleka suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar garin Bangassou da mafi yawansu musulmi ne, inda suka aiwatar da kashe-kashen gilla kan fararen hula da yawansu ya haura 30 gami da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya guda shida.

3600121


captcha