Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da taron yaye daliban hardar kur'ani a makaranta Zaid bin Thabit a birnin Khartum na kasar Sudan.
An gudanar da taron ne tare da halartar Sheikh Mustafa Tamel bababn mai bayar da fatawa na kasar Turkiya, inda aka bayar da takardun shedar kammala hardar kur'ani mai tsarki ga dalibai maza guda 18 sai kuma mata su ma guda 18a wurin.
Muhammad bin Abdullatif shi ne shugaban cibiyar kula da harkokin kur'ani, wanda kuma ya jagoranci shirya wannan taro, ya bayyana cewa sakamakon hadin gwiwa tsakanin malaman Sudan da Turkiya, an kara samun ci gaba ta fuskar ayyuakn kur'ani a kasar.
Ya kara da cewa, an fara gudanar da wannan aiki nahdin gwiwa tsakanin Sudan da Turkiya ne tun shekarar da ta gabata, kuma ya zuwa yanzu an samu daliban Sudan da suka tafi Turkiya domin hardar kur'ani mai tsarki a kasar.