Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na FastCompany cewa, babbar cibiyar musulmin kasar Birtaniya ta fitar da bayani na yin Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a kan jama’a agarin Manchester, wanda ya yi sanadiyyar mustuwar mutane 22 tare da jikkatar wasu da dama.
Bayanin ya ce musulmin kasar Birtaniya na isar da sakon ta’aziyya da alhini ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari, tare da tabbatar musu da cewa, wanann hari ba shi da alaka da addinin muslunci, ko da kuwa wadanda suka shirya hakan sun yi da’awar cewa su musulmi ne, domin idan aka yi la’akari akasarin wadanda suke sakamakon hare-haren ta’addan da irin wadannan mutane suke kaiwa a wasu kasashen gabas ta tsakiya, za a ga cewa musulmi ne suke kashewa a kowace rana, saboda haka basu wakiltar musulmi ko addinin muslunci.
Cibiyar ta ce za ta shirya gudanar da wasu taruka a cikin biranan kasar Birtaniya domin kara wayarwa jama’a da kai hakikanin koyarwar muslunci da ke yin kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin ‘yan adam.