IQNA

Jagora A Hubbaren Imam Khomeini (RA):

Akidar Juyi Ita Ce Jami’ai Kada Su Mika Wuya Ga Manufofin Makiya

23:36 - June 04, 2017
Lambar Labari: 3481579
Banagren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar juyin juya halin Musulunci da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya jagoranta a Iran ya samar wa mutanen Iran mutumci da kuma 'yancin kai, yana mai sake jaddada aniyar al'ummar Iran na ci gaba da riko da tafarkin marigayi Imam.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi wajen bikin tunawa da shekaru 28 da rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) da aka gudanar a hubbaren marigayin da ke nan birnin Tehran inda yace wajibi ne a yi kokari wajen kiyaye koyarwar marigayi Imam Khumainin daga kokarin da wasu suke yi na gurbata shi.

Yayin da yake magana kan irin kalubalen da juyin juya halin Musulunci na Iran din ya fuskanta tsawon shekaru tun bayan nasararsa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar makiyan al'ummar Iran sun gaza wajen cutar da juyin sakamakon tsayin daka da al'ummar Iran din musamman matasa suka yi duk kuwa da matsin lamba da takunkumin da aka sanya wa kasar.

Yayin da yake magana kan irin makirce-makirce da yaudarar gwamnatocin Amurka kuwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar a lokacin rayuwarsa marigayi Imam ya bayyana Amurka a matsayin "babbar shaidaniya wacce ba abar dogaro ba ce" a halin halin yanzu bayan gushewar shekaru sai ga shi shugabannin kasashen Turai suna tabbatar da wannan kalami na Imam da bayyana Amurkan da cewa ba abar yarda ba ce.

Yayin da ya koma kan irin danyen aikin da gwamnatin Saudiyya ta ke yi a kasashen Yemen da Bahrain kuwa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar koda wasa gwamnatin Saudiyyan ba za ta yi nasara a kan wadannan al'ummomin ba.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran ya bayyana takaicinsa dangane da irin rikice-rikice da zubar da jinin da ke faruwa a kasashen musulmi kama daga Siriya, Iraki, Libiya da sauransu wadanda dukkanin hakan wani kokari ne na raunana kasashen musulmi. Kamar yadda kuma Jagoran ya jinjinawa al'ummar Iran dangane da irin fitowar da suka yi kwansu da kwarkwatarsu yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar a Iran yana mai cewa hakan wani lamari ne da ke nuni da riko da tsarin Musulunci da ke iko a kasar Iran din da al'ummar kasar suke yi.

A yau ne ake gudanar da bukukuwan juyayin rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a duk fadin kasar ta Iran inda ake sa ran a yammacin yau Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zai gabatar da jawabi kan hakan a hubbaren marigayi Imam din da ke wajen birnin Tehran.

A wata sanarwa da cibiyar kula da kuma yada ayyukan marigayi Imam Khumaini (r.a) ta fitar ta sanar da cewa taron juyayin tunawa da marigayi Imam Khumainin zai gudana ne a hubbaren nasa a yammacin yau yamma, sabanin yadda aka saba gabatarwa da safe saboda azumin watan Ramalana inda ta ce bikin juyayin na bana, kamar shekarun da suka gabata, za a gudanar da shi ne karkashin jagorancinJagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei wanda zai gabatar da jawabi a wajen.

Baya ga miliyoyin al'ummar Iran da suka hada da manyan jami'an kasar, har ila yau kuma taron dai ya sami halartar baki daga kasashe daban-daban na duniya bugu da kari kan 'yan jarida na ciki da wajen Iran.

A ranar hudu ga watan ga watan yunin shekara ta dubu daya da dari daya da tamanin da tara ne Allah Yayi wa marigayi Imam Khumaini (r.a) rasuwa, shekaru 10 da nasarar da ya samu na jagorantar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran wanda ya fatattaki gwamnatin kama karya ta Shah a kasar. A duk shekara idan wannan rana ta zagayo al'ummar Iran suka gudanar da bukukuwan juyayin wannan babban rashi da aka yi da kuma sake jaddada mubaya'arsu a gare shi da kuma koyarwar da ya bari.

3606322


captcha