IQNA

Gasar Kur’ani Da Nahjul Balagha Ta Mata A Najaf

23:41 - June 04, 2017
Lambar Labari: 3481581
Bangaren kasa da kasa, bangaren kula da harkokin kur’ani a karkashin hubbaren Alawi a birnin ya dauki nauyin gudanar da gasar kur’ani da Nahjul Balagha ta mata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na QAF cewa, Anwar Alhasnawi shugabar bangaren mata a kana bin da ya shafi kur’amni a karkashin cibiyar kur’ani ta hubbaren Alawi ita ce ta jagoranci wannan gasa.

Ta bayyana cewa, babbar manufar gudanar da wannan gasa ita ce yada koyarwar al’kur’ani mai tsarki, a kan haka ne a ka zabi wannan lokaci da ake gudanar da ibadar azukimia cikin wannan wata mai alfarma domin gudanar da wannan gasa ta kur’ani.

Gasar dai an gudanar da ita ne a rubuce, inda aka bayar da tambayoyi da suka danganci wasu lamurra da suka shafi kur’ani, da kuma Karin haske kan wasu abubuwan da kur’ani ya ambata a cikin wasu ayoyi, bayan na kuma an gudanar da gasar a bangaren nahjul balagha.

Ta ce an tanaji wasu kyautuka na musamman da za a bayar ga wadanda suka nuna kwazoa gasar, wanda kuma za a basu ne a lokacin gudanar da taron rufe gasar.

3606409


captcha