Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta
cewa, gidan talabijin na alalam ya nakalto ministar harkokin wajen kasar Qatar
tana fadar haka a safiyar yau Litinin, ta kuma kara da cewa duk zargin kasashen
Saudia, Emarate, Masar da kuma Bahrain suka mata zunzurutun kaayi ne kuma yaki
ne da ita don sabanin da suke da ita a cikin wasu lamura a yankin.
Ma'aikatar da kara da cewa kasar zata ci gaba da aiki tare da kuma mutunta dukkan yerjeniyoyi da suka cimma tsakaninta da kasar yankin Tekun farisa. Sannan zata ci gaba da mutunta 'yencin sauran kasashen yankin.
A jiya Lahadi ne wasu kasashen Larabawa wadanda suka hada da Saudia, Masar, Emmarate da kuma Bahrain suka katsae huldan jakadanci da kasar Qatar, suka dakatar da ziraga zirgan jiragen sama, ruwa da na kasa tsakaninsu da ita,tare da zarginta da goyon bayan ayyukan ta'addanci.