Bayanin Nasa Kamar Haka
Hare hare kan masu azumi wanda yakai wasunsu ga shahada da kuma raunata wasu da dama, yana nuna irin kiyayyar da karnukan farautar manya manyan kasashen duniya da magaya bayansu sukewa mutanen kasar Iran, juyin juya halin musulunci.
Jagoran ya kara da cewa, wannan yana nuna irin mummunan manufar wadanda suka kai hare haren da kuma wadanda sukaumurcesu da yin hakan, sannan hakan ba zai sauya wani abu a matsayin mutanen kasar Iran ba.
Haka nan kuma jagoran ya ce, yana da tabbaci kan cewa sakamakon wadannan harehare ba zai yi kome ba sai dadakyama ga wadanda suka aikata su, musamman musamman Amurka da kasar Saudia.
Ya kammala da cewa ba abinda wadannan hare hare zasu karawa mutanen Iran in banda ci gaba da karin daukaka a duniya.Ya kuma roki Allah Ta'ala ya lullube shahidan wadannan hare hare a da rahamarsa. daga karshe Jagoran yayi bushara ga iyalan shaheedan ya kuma mika ta'aziyyarsa garesu.
Sayyid Ali Khamenei
9/Yuni/2017