IQNA

Taziyyar Cibiyar Kur'ani A Hubbaren Imam Hussain Kan Shahadar Sayyid Taghvi

23:53 - June 09, 2017
Lambar Labari: 3481595
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da harkokin kur'ani a karakashin hubbaren Imam Hussain ta sanar da mika sakon ta'aziyya kan shahadar Hojjatol Islam Sayyid Mahdi Taghvi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sakon na cibiyar kur'ani ta hubbaren Imam Hussain (AS) yana dauke da sanarwar cewa, mun samu labari da ya sanya mu a cikin bakin ciki kan shahadar Sayyid Mahdi taghvi tsohon shugaban IQNA, sakamakon hare-haren 'yan ta'adda.

Bayanin ya ce ko shakka babu wannan mutum mai kokari da himma wajen yada sakon kur'ani, rashinsa a tsakanin al'ummar musulmi babban rashi ne maras misiltuwa, a kan haka cibiyar tana isar da sakon ta'aziyya ga al'ummar Iran da kuma danginsa da iyalansa baki daya.

Tare da yin fatan Allah madaukakin sarki ya yi masa rahma ya hada shi da masoyansa daga iyalan gidan manzo, wadanda suka yi shahada tare da shi Allah ya jikansu, ya kuma baiwa wadanda suka samu raunuka sauki.

Hojjatol Islam Sayyid Mahdi Taghvi ya yi shahada ne a ranar Talata da ta gabata a cikin babban ginin majalisar dokokin Iran, a lokacin da 'yan ta'addan takfiriyya suka kai hari a wurin.

3607640


captcha