IQNA

Wakilan Kasashen 53 A Gasar Kur’ani Ta Aljeriya / Muhammad Ali Islami Wakilin Iran

23:49 - June 11, 2017
Lambar Labari: 3481602
Bangaren gasar kur’ani, za a gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya a kasar Aljeriya nan da mako guda mai zuwa tare da halartar wakilai daga kasashe 53 na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, tashar radiyo Algeria ta bayar da rahoton cewa, Nuruddin Muhammadi shugaban shugaban bangaren kula da harkokin kur’ania ma’aikatar kula da addini ta kasar Aljeriya ya bayyana cewa, a ranar ashirin da biyu ga wannan wata na Ramadan ne za abude gasar kur’ani ta duniya karo na sha hudu a kasar ta Aljeriya.

Ya ce wannan gasa ana gudanar da ita tun 2003 karkashin kulawar shugaban kasar Abdul aziz Butaflika,kuma za ta samu halartar wakilai daga kasashen duniya 53 da suka hada da mahardata da kuma makaranta, inda za su kara da juna a dukkanin bangarori na gasar, dsa suka hada da harda da kuma karatun kur’ani mai tsarkida kuma hukuncin karatun wato tajwidi.

Haka nan kuma yayi nuni da cewa akarshen gasar za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo, daga matsayi na daya zuwa na uku, inda za abayar da dinari miliyan daya ga mutum na farko, dinari dubu 800 ga mutum na biyu, dinari dubu 500 ga mutum na uku.

A bangaren gasar da ta kebanci yara ma haka lamarin yake, za a bayar da kyautuka nan a farko dinari dubu 600, na biyu kuma dinari dubu 400 sai kuma na uku dinari dubu 200.

Muhammad Ali Islami zai wakilici Iran, yayin da Muhammad Reza Setuden niya zai raka shi.

3607994


captcha