IQNA

An Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Matasa A Ghana

23:51 - June 17, 2017
Lambar Labari: 3481618
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar karatu da kuma hardar kur'ani ta kebanci matasa akasar Ghana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ofishin kula da harkokin al'adu na jahuriyar muslunci ta Iran ya dauki nauyin shirya gasar kur'ani a kasar Ghana a lokacin da ake raya dararen lailatun qadr.

A yayin wannan gasa an raba masu gasa zuwa kashi uku da suka hada da bangaren harda da kuma karatu sai kuma bangaren hukuncin karatu, inda a kowane bangare an kara tsakanin matasan.

Muhammad Hassan shugaban ofishin kula da harkokin al'adu na kasar Iran a kasar Ghana wanda ya shiga gaba domin gudanar da wannan gasa ya bayyana cewa, kasar Ghana tana da matasa wadanda suke himma da kwazo kan batun addini, a kan haka ya zama a ci gaba da basu horo a kan kur'ani musamman bangaren harda da karatu.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin taron gasar ya bayyana cewa, kur'ani mai tsarki shi ne littafin da ya hada dukaknin msuulmi, a kan haka dole ne musulmi ya rike kur'ani a duk inda yake, ba ta hanyar karatu ko hard aba kawai, ta hanyar wadannan abubuwan biyu da kuma aiki da abin da ya kunsa.

Daga karhe an bayanr da kyautuka ga dukaknin wadanda suka halarci gasar, hakan nan an bayar da wasu kyautukan na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

3610513


captcha