Wani jami'in tsaro ya bayyana cewa, dukkanin 'yan matan biyu sun mutu, sun kuma kashe wasu da suka hada da masu salla da kuma mai gadi.
Jami'in ya kara da cewa, ba a wuce mako guda ba tare da 'yan ta'addan Boko haram sun kaddamar da hare-hare makamanta irin wannan ba, da hakan ya hada da masallatai da kuma wuraren tarukan jama'a kamar kasuwanni da sauransu.
Daga watan June da ya gabata na wanann shekara ta 2017 ya zuwa yanzu mutane 20 ne suka rasu sakamakon irin wadannan hare-hare na ta'addanci.
Wani rahoton majalisar dinkin duniya ya tabbatar da cewa, tun daga lokacin da 'yan ta'addan suka fara kaddamar da irin wadannan hare-hare ya zuwa yanzu sama da mutane miliyan 26 ne suka kaurace ma yankunansu a cikin cikin kasashen da ke makwabtaka da tafkin Chadi.