Taron dai ya gudana ne tare da halartar masana da kuma lauyoyi gami da wasu 'yan siyasa da kuma wakilan kungiyoyin kare hakkin bil adama da ma sauran musulmi daga wasu birane na kasar.
Kamar yadda aka saba taron yakan duba wasu daga cikin muhimamn lamurra da suka shafi musulmi domin yin dubi a kansu a kowace shekara, inda akan saurari jawabai da kuma shawarwari daga mahalarta, sai dai a wannan karon taron ya mayar da kakkausan martani kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka wanda ya samu amincewar kotun koli, na hana wasu daga cikin musulmi shiga kasar.
Kasashen da Aurka ta dauki wanann mataki a kansu dai sun hada da Iran, Somalia, Syria, Yemen, Sudan da kuma Libyam wanda kuma yana daga cikin salon siyasar gwamnatin da ke mulki a halin yanzu da ta shahara tun lokacin yakin neman zabe a kan tsananin kiyayya da musulmi.
Musulmin Amurka sun bayyana wannan mataki na gwamnatin Trum a matsayin nuna wariya da kyama ga musulmi.
Yawan muuslmin Amurka a halin yanzu yana atsakanin miliyan 5 zuwa miliyan 8a fadain kasar.