IQNA

Mafi Tsadar Dan Wasan Kwallon Kafa Yana Kare Addinin Muslunci

23:35 - July 02, 2017
1
Lambar Labari: 3481664
Bangaren kasa da kasa, Paul Pogba dan wasan kwallon kafa a babbar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya nisanta duk wani akin ta’addanci da addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Teleghraph ta bayae da rahoton cewa, Pogba ya nisanta addinin muslcni da duk wani aikin ta’addanci.

Wannan kuwa yana zuwa ne biyo bayan harin ta’addancin da aka kai a birnin Manchester wanda wasu ‘yan ta’adda masu dauke da akidar wahabiyanci ‘yan kungiyar daesh suka kaddamar, inda suka kasha tare da jikkata mutane da dama.

Ya ce ko shakka babu duk wanda zai aikata wani aki irin wannan da sunan muslunci to hakika muslucni ya barranta daga gare shi da aikinsa, domin addinin muslunci addini na girmama dan adam da kare rayuwarsa da mutuncinsa, a kan haka ‘yan ta’adda ba su wakiltar muslunci koda sun kira kansu musulmi.

Pogba wanda ke buga wasa akungiyar kwallon kafa ta Manchester, yana daga cikin ‘yan wasa da taurarinsu ke tashe a duniya, wanda kuma dan kasar Faransa da iyayensa suka hijira daga kasar Guinea zuwa Faransa, inda aka haife shi a kusa da birnin Paris a cikin shekara ta 1993.

3614439


Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Assalamu alaikum dubun gaisuwa mai yawa zuwaga pawul foba wasika daga ustas abdullahi abubaka r
captcha