IQNA

Daya Daga Cikin Dadaddun Masallatai Na Fuskantar Rushewa A Kenya

23:50 - July 15, 2017
Lambar Labari: 3481703
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin masallatan musulmi mafi dadewa a duniya da ke yankin Mawapa a kasar Kenya na fskantar barazanar rushewa saboda rashin kula.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na standardmediacewa, cibiyar kula da adana kayan tarihi ta kasar Kenya NMK ta sanar da cewa, wannan masallaci da aka gina tun shekaru 500 yana fuskantar barazana ta rushewa, saboda yadda aka bar shi ba tare da kula ba.

Bayanin cibiyar yace wurare irin wadannan masu matukar muhimmanci a tarihin kasar bai kamata mahkunta su sanya idi su lalace ba, domin kuwa irin wadannan wurare su ne kimarr kasar Kenya da tarihinta.

Babbar cibiyar kula da adana kayan tarihia kasar Kenya dai ta saka wannan wri a cikin muhimamn wuraren tarihi na kasar wadanda suke da matsayi na musammana tarihinta.

An gina wannan masallaci tun a cikin shekara ta 1500 miladiyya, kuma sakamakon rashin gyara da kulawa yadda ya kamata, ya sanya zafin rana da kuma ruwan sama, suna zaizaye ginin masallacin, wanda a cewar hukuma, zai iya rushewa matukar dai ba dauki mataki ba.

3618923


captcha