Wanann yana daga cikin ayyukan da cibiyoyin da ke gudanar da ayyukan alkhairi a yankin suke gudanarwa tare da taimakon wasu daga cikin kasashen larabawan yankin tekun fasha.
Abdulrazaq Adam Shari y ace babbar manufar gudanar da wannan aiki ita ce karfafa gwiwar daliban makarantu na yankin, usamman ma ganin cewa yanki ne wanda ya kunshi musulmi da suke bayar da muhimamnci ga lamarin kur'ani.