IQNA

An Bude Kofar Imam Sadiq (AS) A Hubbaren Alawi

20:33 - July 21, 2017
Lambar Labari: 3481721
Bangaren kasa da kasa, a ranar shahadar Imam Sadiq (AS) an bude wata kofa mai suna kofar Imam Sadiq (AS) a hubbaren Alawi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo bangaren hulda da jama'a na hubbaren Imam Ali (As) cewa, an bude wata kofa mai suna kofar Imam Sadiq (AS) domin shigar mata zalla.

Manal Hussain ita ce mai kula da lamurran da suka danganci mata a hubbaren mai tsarki, ta bayyana cewa suna mika godiya ga Allah madaukakin sarki da ya nuna musu wannan rana da aka samu damar bude wannan wuri.

Ta ce ko shakka babu bude wannn babbar kofa zai taimaka matuka wajen rage yawan cunkoson da ake fuskanta a wurin, musammana lokutan tarukan addini.

3621248


captcha