IQNA

Shugaba Rauhani Ya Yi Rantsuwar Kama Shugabanci Wa'adi Na Biyu

21:11 - August 05, 2017
Lambar Labari: 3481768
Bangaren siyasa, shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya yi rantsuwar kama shugabancin kasar a wa'adi na biyu.
Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, a yau ne shugaban kasar Iran Hassan Rauhani zai yi rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adin shugabancin kasar Iran na biyu, bayan da aka gudanar da taron tabbatar da shi daga bangaren jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei a ranar Alhamis da ta gabata.

A lokacin da ya gabatar da jawabinsa a ranar Alhamis da ta gabata a wurin taron tabbatar da shi, Dr. Rauhani ya bayyana cewa, Iran za ta ci gaba da kyautata alakarta da dukkanin kasashen duniya, a bangarori na siyasa, tattalin arziki, tsaro, al'adu da dai sauransu, duk kuwa da irin da matakan da sabuwar gwamnatin Amurka take dauka na kokarin ganin ta mayar da Iran saniyar ware, wanda ya ce hakan ba zai nasara ba.

Haka na kuma a bangaren ayyukan da zai mayar da hankali a kansu, Rauhani ya bayyana cewa, gudanar da ayyukan ci gaban kasa da bunkasa ilimi a dukaknin fagage na kimiyya da fasaha da kere-kere da karfafa kamfanoni da masana'antu na cikin gida domin samar da guraben ayyukan yi ga matasa musamman, na daga cikin abubuwan da zai kara mayar da hankali a kansu.

Haka nan kuma Rauhani ya bayyana cewa, a daidai lokacin da gwamnatinsa take karfafa ayyukan dogaro da kai na cikin gida, kofa bude take ga gwamnatoci ko daidaikun 'yan kasuwa ko kamfanoni masu saka hannayen jari na kasashen ketare a bangarorin daban-daban da za su iya yin aiki tare da Iran.

Wannan dai shi ne karo na 12 da zababben shugaban kasa zai sha rantsuwar kama aiki a wa'adin shugabanci a kasar Iran, tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar.

3626992


captcha