Wadannan taruka dai8 sun hada da gudanar da jawabai da malamai suke yi, kan matsayin Imam Ridha (AS) da kuam sauran limaman ahlul bait, da kuma irin darussan da al'ummar musulmi za su iya dauka daga rayuwarsu mai albarka.
Baya ga jawabai, an gudanar da wakokin yabo ga manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka da kuma Imam Ridha da sauran limaman ahlul bait, amincin Allah ya tabbata a gare su.
Daga cikin muhimman biranan da aka gudanar da irin wadannan taruka masu albarka, akwai biranan Karachi, lahour, Kuita Bishawur da kuam Baluchestan da sauransu, inda al'umma suke cike da farin ciki a kan zagayowar wannan rana.
Wuraren da ak gudanar da tarukan dai mafi yawa masallatai ne, sai kuma wuraren gudanar da taruka na addini da ma manyan dakunan taruka a manyan birane.
Jama'a suna bayar da halwa domin taya sauran al'ummar msuulmi murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka.