IQNA

Trump Ya Yi Shiru kan Harin da Aka Kaiwa Musulmi A Minnesota

23:58 - August 10, 2017
Lambar Labari: 3481785
Bangaren kasa da kasa, dan majalisar dokokin kasar Amurka musulmi daga jahar Minnesota ya yi suka kan yadda Trump ya yi gum da bakinsa dangane da harin da aka kai wa cibiya da masallacin musulmi.
Trump Ya Yi Shiru kan Harin da Aka Kaiwa Musulmi A Minnesota

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ahfin yada labarai na theglobeandmail ya habarta cewa, Keith Ellison dan majalisar dokokin kasar Amurka mai wakiltar jahar Minnesota wanda kuma msuulmi ne daga cikin musulmin jahar, ya yi kakkausar danganr da yadda shugaban kasar Amurka yaki y ace ffan kan harin da aka kai wa masallacin musulmi a jahar ta Minnesota.

Ya ce shiru da Trump ya yi dangane da wannan hari ya nuna cewa yana nuna banbanci a tsakanin al’ummar Amurka, domin kuwa dukkanin hare-haren da aka kai na ta’addanci a cikin Amurka da wasu kasashen turai duk yak an yi Allah wadai da hakan, amma harin ta’addanci da aka kai a kan masallacin musulmi a Amurka ba abin yin Allah wadai ba ne a wurin Trump.

Daga karshe dan majalisar dokokin kasar ta Amuka ya bukaci Trump da ya fito fili ya bayyana ma al’ummar Amurka matsayinsa a kan harin da aka kai kan cibiyar musulmi da masallacinsu a jahar Minnesota.

A cikin makon da ya gabata ne dai wasu da ba san ko su wanene ba suka jefa wasu abubuwa masu tarwatsewa acikin masalalcin Minnesota a lokacin da ake sallarr asubahi, amma dai babu wanda ya rasa ransa, lamarin da ke ci gaba da fuskantar Allah wadai daga al’ummomi da daa a kasar ta Amurka.

3628871

captcha