Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, ya nakalto daga tashar Press TV cewa, al'ummomin kauyen Zay Di Pyin da ke
jihar Rakhine din suna fadin cewa kimanin musulmi 700 ne 'yan Buddha suka
killace su da hana su fita zuwa aiki ko zuwa kasuwa don sayen abubuwan da suke
bukata bugu da kari kan hana su ruwan sha.
Kungiyoyi masu sanya ido da kuma kai agaji na kasa da kasa da suke kasar ta Myammar dai sun tabbatar da wannan labarin inda suka ce masu tsaurin ra'ayin sun killace musulmi a yankin ta yadda ba su da wata hanya ta samun abubuwan da suke bukata na rayuwar yau da kullum.
Wannan yanayin dai shi ne zalunci na baya-bayan nan da 'yan Budha masu tsaurin ra'ayi da suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Myammar din suke yi wa musulmin Rohingya din wadanda sun kai mutane miliyan guda suke rayuwa a yankunan arewacin kasar.