IQNA

Kotu Ta Daure Mai Cin Zarafin Musulmi Shekaru 16 A Gidan Kaso

23:55 - August 29, 2017
Lambar Labari: 3481845
Bangaren kasa da kasa, Wata kotu a jahar California a kasar Amurka ta yanke hukunci daurin shekaru 16 a kan wani mutum da ya kai hari a kan musulmi a wani masallaci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai Keyt ya bayar da rahoton cewa, kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 16 a kan Marco Antony Dalakoza da shekaru 27 da ya kai hario wani masallaci a garin Simi Vally na jahar Californi a akasar Amurka.

Mutumin yan kai harin ne tare da wani abokinsa mai John Watson dan sheka 29a cikin watan Disamban da ya gabata, inda suka shiga masallacin suka ci zarafin musulmi, daga bisani kuma Dalakoza ya daba wa wani masallaci wuka.

Jami'an tsaro sun gurfanar da shi da bisa zargin kawo tashin hankali a cikin kasa, da kuma kai haria wurin ibada gami da yunkurin kashe wani saboda banbancin addini.

Yanzu haka dai ana jiran ganin shari'ar abokin nasa wanda shi ma tuni aka cafke shi, kuma zai gurfana a gaban kuliya.

3635952


captcha